Isa ga babban shafi
Wasanni

An yi jana'izar Diego Maradona

An yi jana’izar tsohon dan wasan Argentina Diego Maradona a birnin Buenos Aires na kasar Argentina.A lokacin wannan jana'izar an fuskanci arrangama da ta kaure tsakanin magoya bayan Maradona da yan Sanda dake kula da tsaro.

Marigayi Diego Armando Maradona ,tsohon dan wasan Argentina
Marigayi Diego Armando Maradona ,tsohon dan wasan Argentina REUTERS/Henry Romero
Talla

An gudanar da jana-izar tsohon dan wasan Argentina marigayi Diego Armando Maradona a makabartar Buenos Airos kwana daya bayan mutuwar sa, a wannan wuri da aka sani da lambun zaman lafiya ko jardin de la paix ,inda aka bine mahaifan sa.

Yan lokuta kafin bine tsohon dan wasan,jama’a sun yi tattaki zuwa wurin da aka ajiye akwatin gawar don yi masa bankwanan karshe, yayinda lauyan sa a jiya alhamis ya bayyana takaicin sa da rashin ko in kula daga direbobin motocin rashi lafiya da suka iso a makare don kai dauki ga marigayi Diego Maradona.

Lauyan ya bayyana cewa tsawon sai da aka kusa share sa’o’I 12 ba a samu wani jami’in kiwon lafiya da ya ziyarci mamaci,banda haka motar marar sa lafiya ta share kusan rabi awa ba tareda sun samu isowa bayan kiran da aka musu.

Lauyan mai suna Matias Moria ya bayyana bakin cikin sa,da kuma danganta mamacin a matsayin mutun mai hange nisa da ya rasu bayan fama da bugun zuciya ya na mai shekaru 60 a Duniya.

A filayen wasani daban-daban an share yan lokuta tareda yi shuru don girmama mamaci.

Sai dai an samu arrangama tsakanin jami’an tsaro da magoya bayan Maradona a lokacin da aka kama hanya zuwa makabarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.