Isa ga babban shafi
Afrika

Mutane 17 ne suka salwanta bayan rushewar gini a Ghana

Akalla mutane 17 ne suka salwanta wasu gommai kuma ake kyautata zaton sun makale a cikin buraguzan ginin wata coci mai hawa uku da ta ruguje a yankin gabashin kasar Ghana a cewar hukumomi a kasar.

Faduwar bene da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama
Faduwar bene da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama Punch
Talla

Majiyar masu aikin ceto sun tabbatarwa kamfanin dilancin labaren Faransa AFP cewa, an yi nasarar zaro mutane 8 da rai, a yayin da wasu 17 kuma sun riga mu gidan gaskiya.

Mai kula da shugabancin hukumar ayukan jinkan kasar ta Ghana Gyan Willington ya ce, yanzu haka sun aika da karin ma’aikata da nufin kauda buraguzan ginin bisa fargabar cewa akwai mutane da dama cikin ginin .

A nasa bangaren gwamnan yankin gabashin kasar ta Ghana Eric Darfour ya sanar da AFP cewa, an garzaya da mutanen da suka jikkata a asibiti. ya kuma kara da cewa a halin yanzu basu da wata masaniya ta adadin mutanen da ke ci gaba da kasance makale a karkashin baraguzan ginin, amma duk da haka masu aikin ceto na ci gaba da kokarin da suke na ganin sun samo masu sauran numfashi

kawo yanzu dai babu wani bayanin dangane da dalilin faruwar hatsarin

shaidun da suka tsira daga hatsarin sun sanar da cewa, sama da mutane 60 ne ke gudanar da taron ibada a lokacin da ginin cocin mai hawa 3 ya ruguje a garin Akyem Batabi.

Mavis Antwi ya ce suna hutawa ne a ciki lokacin da wani sashen ginin ya fara riftawa. inda suka bazama, kowa na kokarin fita, ya samu ya fice tare da wasu dadama amma kuma an rutsa da wasu yanzu haka

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.