Isa ga babban shafi
Libya

Libya: Bangarorin da ke rikici sun koma teburin tattaunawa

Majalisar Dinkin Duniya ta ce bangarorin da ke kai ruwa rana da juna a rikicin kasar Libya sun sake komawa teburin tattaunawa a  Litinin din nan a Geneva, a kokarin da suke na kawo karshen zub da jini da aka kwashe gwamman shekaru ana yi.

Shugaban gwamnatin hadin kan Libya, Fayez el-Sarraj.
Shugaban gwamnatin hadin kan Libya, Fayez el-Sarraj. REUTERS/Ismail Zitouny
Talla

Libya dai ta fada cikin rikici tun lokacin da kungiyar tsaro ta NATO ta jahgoranci wani tada zaune tsaye da ya yi sanadin rugujewar gwamnatin shugaba Moamer Gaddafi.

Tun daga wannan lokacin ne kungiyoyi masu dauke da makamai suka mamaye kasar, lamarin da ya haddasa rikicin cikin gida tsakanin kungiyoyi dabam dabam.

Amma an samu kwarin gwiwar lalubo mafita a game da rikicin, lokacin da bangarori biyun da ke ba hammata iska suka sanar da aniyarsu ta dakatar da rikici a watan Agusta, sai dai dukkannin bangarorin na zargin juna da goyon bayan kungiyoyin ta’addanci.

Gwamnatin hadin kan kasa mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya a karkashin jagorancin Fayez al-Sarraj, mai mazauni a Tripoli, na fuskantar kalubale daga janar din soji mai tada kayar baya, Khalifa Haftar.

Tattaunawar lalubo zaman lafiyar, wacce majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta, tana aiki ne da wakilai 5 daga dukkan bangarori.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.