Isa ga babban shafi
Afrika-Libya

Kungiyar Turai ta yaba da tsagaita wutar da aka samu a Libya

Kungiyar Turai ta yaba da tsagaita wutar da aka samu a Libya tsakanin bangarorin da basa ga maciji da juna wanda zai bada damar gudanar da zaben kasa baki daya. Babban jami’in diflomasiyar kungiyar Josep Barrell ya bayyana matakin a matsayin gagarumar cigaba wanda ya nuna aniyar shugabannin Libya na kawo karshen tankiyar da aka samu domin bude sabon babin da zai kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Dakarun gwamnatin hadin gwiwa a Bengazhi na kasar Libya
Dakarun gwamnatin hadin gwiwa a Bengazhi na kasar Libya Abdullah DOMA / AFP
Talla

Joseph Barrell Babban jami’in diflomasiyar kungiyar Turai ya bukaci daukar kwararan matakai domin tabbatar da tsagaita wuta na din-din-din, kuma bude kofar tattaunawa tsakanin bangarorin biyu tare da bukatar ficewar sojojin haya da na kasashen waje dake cikin Libya yanzu haka.

Babban jami’in ya kuma bukaci bangarorin biyu su kaddamar da shirin farfado da tattalin arziki wanda zai tabbatar da raba arzikin kasa ga kowanne bangare musamman daga kudaden sayar da man da ake samu.

Kasar Libya ta fada cikin tashin hankali tun bayan shekarar 2011 da Yan tawaye suka kasha shugaba Moammar Ghadafi da taimakon kungiyar NATO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.