Isa ga babban shafi
Afrika

Shugaban Afrika ta tsakiya ya bayyana takarar sa a zaben kasar

Shugaban Afrika ta Tsakiya Faustin Archange Touadera a yau asabar ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takara a babban zaben kasar na ranar 27 ga watan disemba na shekarar bana.

Faustin-Archange Toudéra Shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
Faustin-Archange Toudéra Shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Ludovic MARIN / AFP
Talla

Kasar ta Afrika ta tsakiya tsawon kusan shekaru 7 ta share ana fama da yakin basassa,inda kungiyoyi dauke da makamai suka kama kusan rabin kasar a lokacin.

Watan fabrairu shekarar 2016 ne aka zabi shugaban kasar Faustin Archange Touadera mai shekaru 63a Duniya , wanda ya kuma sake bayyana aniyar sa ta sake tsayawa takara a gaban magoya bayan sa na MCU a babban birnin kasar dake Bangui.

Ana sa ran tsohon Shugaban kasar Francois Bozize da ya dawo kasar kusan shekara daya ya kasance babban dan adawa ga shugaban kasar har indan kotun koli ta amince da takarar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.