Isa ga babban shafi
Afrika-Coronavirus

Kasashen Afrika za su jima basu murmure daga shakar coronavirus ba - Kwararru

Ministan kudin Ghana Ken Ofori-Atta, yace tattalin arzikin kasashen kudu da saharar Afrika zai shafe akalla shekaru 3 bai farfado daga shaker mutuwar da annobar COVID-19 ta yi masa ba.

Ministan kudin Ghana Ken Ofori-Atta
Ministan kudin Ghana Ken Ofori-Atta Modern Ghana
Talla

Har yanzu dai yankin na kudu da saharar Afrika shi ne inda annobar ta COVID-19 ta halaka adadin rayuka mafi karanci a duniya, sai dai kididdiga ta tabbatar da cewar, tasirin annobar ya yiwa tattalin arzikin yankin mummunar illa, yanayin da ya kara muni sakamakon matakan hana zirga-zirga gami da rufe kamfanoni, kasuwanni da ma’aikatu da gwamnatocin kasashe suka yi, domin dakile yaduwar cutar.

A watan Yuli bankin Afrika ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin nahiyar zai soma farfadowa a shekarar 2021 daga magagin tasirin annobar coronavirus, sai dai duk da haka gwamnatocin nahiyar za su tafka hasarar akalla dala biliyan 250 na kudaden shiga.

Yanzu haka dai kusan mutane dubu 30 cutar ta corona ta halaka a nahiyar Afrika, daga cikin kusan mutane miliyan 1 da dubu 250 da suka kamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.