Isa ga babban shafi
Afrika-Coronavirus

'Yan Afrika miliyan 80 na cikin hatsarin shiga kangin talauci bayan COVID-19

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo da tsohon Fira Ministan Habasha Desalegn Boshe, sun gargadi gwamnatocin kasashen Afrika dasu mayarda hankali wajen inganta samar da abinci, ayyukan noma da kuma raya yankunan karkara, a matsayin martanin da za su maidawa annobar coronavirus.

Yankin Mabella dake wajen Freetown, babban birnin kasar Saliyo. 13/3/2008.
Yankin Mabella dake wajen Freetown, babban birnin kasar Saliyo. 13/3/2008. REUTERS/Katrina Manson
Talla

Tsaffin shugabannin biyu, sun yi gargadin ne cikin kasidar da suka wallafa a shafin yanar gizon gidauniyar bunkasa ayyukan noma ta kasa da kasa yau Alhamis.

Obasanjo da Boshe sun yi gargadin Afrika ka iya zama nahiyar da za ta fi kowace a duniya, fuskantar radadin karayar tattalin arzikin da annobar COVID-19 ta haddasawa duniya.

Gargadin yace muddin gwamnatocin Afrika suka ki daukar matakan da suka dace, abinda zai biyo baya bai zai yi kyawu ba, domin kuwa hasashen kwararru ya nuna cewar, rashin daukar matakan rigakafin, zai jefa akalla mutane miliyan 80 cikin kangin talauci a nahiyar ta Afrika, bayan kawo karshen annobar coronavirus a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.