Adadin masu Coronavirus a Afrika ta Kudu ya zarce dubu 500
Yanzu adadin wadanda cutar coronavirus ta harba a Afrika ta Kudu ya zarta dubu dari 5, bayan da ma’aikatar lafiyar kasar ta sanar a daren Asabar cewa mutane dubu dari 5 da 3, da dari 2 da 90 ne gwaji ya tabbatar su harbu da cutar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wannan ya dora kasar a matsayin inda wannan cuta ta fi yin ta’adi, inda fiye da rabin wadanda cutar ta kama a nahiyar Afrika a cikinta suke.
Ya zuwa yanzu, mutane dubu 8 da dai da 53 ne cutar ta kashe, sai dai masu bincike na cikin gida na cewa adadin na iya zarce haka.
Afrika ta Kudu na daga cikin kasashen da ke da bangaren lafiya maai inganci a nahiyar Afrika, ama kuma duk da haka sai da wannan cuta ta buwaye ta sakamakon rashawa da samar da kayayyakin kariya ga ma’aikatan lafiya a asibitocin gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu