Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

'Yan Afrika ta Kudu sama da dubu 1 sun kamu da coronavirus cikin sa'o'i 24

Hukumomin lafiya a Afrika ta Kudu sun ce mutane dubu 1 da 160 sun kamu da cutar coronavirus a rana guda, adadi mafi girma da kasar ta gani tun bayan bullar annobar cikinta a watan Maris.

Daya daga cikin likitoci a Afrika ta Kudu yayin gwajin cutar coronavirus a Jeppestown dake birnin Johannesburg. 14/5/2020.
Daya daga cikin likitoci a Afrika ta Kudu yayin gwajin cutar coronavirus a Jeppestown dake birnin Johannesburg. 14/5/2020. AFP
Talla

A ranar asabar da ta gabata mutane 263 suka kamu da cutar a Afrika ta Kudu, abinda ke nuna cewar zuwa ranar lahadi adadin ya ninkasama da sau 4.

Ma’aikatar lafiyar kasar tace a halin yanzu jumillar yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar ya kai dubu 15 da 515, daga cikin kuma 264 sun mutu.

Afrika ta Kudu ta fi kowace kasa yawan masu cutar coronavirus a nahiyar Afrika, biye da ita Masar ce mai mutane dubu 11 da 719 da suka kamu, daga cikinsu kuma 612 sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.