Isa ga babban shafi
Afrika

Wani alkali a Ghana ya killace kan sa sabili da covid 19

Alkalin Alkalan Ghana Kwasi Anin Yeboah ya zama daya daga cikin fitattun yan Afirka da suka killace kan su sakamakon rahotan kamuwa da cutar coronavirus da wasu alkalan kasar suka yi.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo. Paul Marotta/Getty Images
Talla

Rahotanni daga Ghana sun ce Alkalin Alkalan ya fara killace kan sa daga ranar laraba, kuma zai kwashe kwanaki 14 kamar yadda hukumomin lafiya suka bada shawara.

Shima shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Ado ya killace kan sa daga karshen makon da ya gabata, inda yake gudanar da aikin sa daga gida.

Rahotanni sun ce ya zuwa yanzu mutane 21,968 sun kamu da cutar a Ghana, yayin da ta kashe 129.

Wasu kasashen Afrika na iya kokarin su don dakile yaduwar Coronavirus,yayinda kasashe kamar su Madagascar da Morocco suka aiwatar da dokar sake killace yan kasar su bayan bulluwar cutar a yankunan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.