Isa ga babban shafi
Libya

Sau 17 aka kaiwa cibiyoyin lafiya hare-hare a 2020 - MDD

Majalisar Dinkin Duniya tace sau 17 dakarun Janar Khalifa Haftar dake kokarin kwace iko da birnin Tripoli a Libya, ke kai hare hare kan asibitoci da kuma cibiyoyin kula da lafiya a cikin wannan shekara.

Gwamnatin Libya ta dora alhakin jerin hare-haren da ake kaiwa asibitoci kan dakarun Janar Khalifa Haftar.
Gwamnatin Libya ta dora alhakin jerin hare-haren da ake kaiwa asibitoci kan dakarun Janar Khalifa Haftar. Getty Images
Talla

Ofishin Majalisar ya bayyana haka ne bayan harin baya bayan nan da dakarun Haftar suka kai kan babban asibitin Tripoli a ranar alhamis da ta gabata.

Mai Magana da yawun ma’aikatar lafiyar kasar Amin al-Hashemi ya tabbatar da harin wanda yace ya lalata cibiyar kula da lafiyar da sashen yaki da cututtuka masu yaduwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana bacin ran ta da yadda dakarun Haftar ke kai hare hare kan fararen hula wanda ke matukar illa ga duk wani yunkuri na sasanta rikicin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.