Isa ga babban shafi
Coronavirus

Coronavirus ta kashe tsohon firaministan Libya

Cutar Coronavirus ta kashe tsohon firaministan kasar Libya Mahmud Jibril, wanda ya jagoranci gwamnatin ‘yan tawayen da suka hambarar da Kanar Gadhafi daga karagar mulki a 2011.

Tsohon firaministan Libya Mahmoud Jibril da coronavirus ta kashe a Masar.
Tsohon firaministan Libya Mahmoud Jibril da coronavirus ta kashe a Masar. REUTERS/Zohra Bensemra
Talla

Jibril mai shekaru 68 a duniya, ya mutu ne yau ne Lahadi a birnin Alkahira na kasar Masar, kamar dai yadda sakataren jam’iyyarsa Khaled al-Mirimi ya tabbatar.

Marigayin ya shafe tsawon makwanni biyu yana jinya a asibitin birnin Alkahira.

Shi kuwa Sarki Mohammad na 6 na kasar Maroko, a ya bayar da umarnin sakin fursunoni dubu 5 daga gidajen yarin kasar, daya daga cikin matakai don rage cunkoso a wannan lokaci da ake yaki da cutar ta Covid-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.