Isa ga babban shafi

Kuto na tuhumar wasu masu dauke da coronavirus da yunkurin kisa

Yan Sanda a kasar Afirka ta kudu sun gurfanar da wasu mutane biyu a gaban kotu dake dauke da cutar coronavirus amma suka ki killace kan su inda suke tuhumar su da laifin yunkurin kisan kai wajen shirin yada cutar.

Yankin Musina da ke kan iayakar Afirka ta Kudu da Zimbabwe
Yankin Musina da ke kan iayakar Afirka ta Kudu da Zimbabwe WIKUS DE WET / AFP
Talla

Ministan 'yan Sanda Bheki Cele ya bayyana tuhumar lokacin da yake ganawa da manema labarai, inda ya bayyana cewar duk wanda ya karya dokar hana fitar da aka saka a kasar zai gamu da daurin watanni 6 ko kuma biyan tara, ko kuma a hada duka biyu.

Kakakin rundunar 'yan Sandan kasar Vish Naidoo yace mazauna unguwar da mutanen suke ne suka tseguntawa 'Yan sanda cewar mutanen sun ki killace kan su.

Yanzu haka sama da mutane 709 suka kamu da cutar a Afirka ta kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.