Isa ga babban shafi
Najeriya-Amurka

Najeriya ta kaddamar da bincike kan dalilan hana 'yan'yanta shiga Amurka

Gwamnatin Najeriya tasanar da kafa kwamitin bincike kan dalilan da suka sanya Amurka daukar matakin haramtawa ‘yan ci rani daga kasar shiga cikinta.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin ganawa da takwaransa na Amurka Donald Trump a birnin Washington. 30/04/2018.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin ganawa da takwaransa na Amurka Donald Trump a birnin Washington. 30/04/2018. AFP
Talla

A Juma’ar nan ce dai 31 ga Janairun 2020, Amurka ta sanar da haramtawa ‘yanci rani daga wasu kasashe 6 shiga cikinta, da suka hada da Najeriya, Tanzania, Sudan, Eritia, Kyrgystan da kuma Myanmar.

Bayan daukar matakin, Amurka ta bayyana rashin cika wasu ka’idoji kan tsaro da musayar bayanai kan lamurran ‘yan ci ranin, da kuma kare 'yancin dan adam, a matsayin dalilan da suka sanya ta daukar matakin kan karin kasashen da suka kunshi 4 daga nahiyar Afrika.

Dokar dai za ta soma aiki ne daga ranar 21 ga Fabarairun 2020.

A shekarar 2017 dai haramcin baiwa baki damar shiga Amurka ya shafi kasashe bakwai ne, da suka hada da, Syria, Yemen, Somalia, Iran, Libya, Korea ta Arewa, da kuma Venezuela.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.