Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu a Najeriya ta daure tsohon gwamna shekaru 12

Wata babbar kotu a birnin Lagos a Tarayyar Najeriya, ta yanke wa sanata mai ci, kuma tsohon gwamnan jihar Abia Orji Uzor Kalu hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari, bayan samun sa da laifin kwanciyar magirbi kan dukiyar al’umma da ta zarce naira biliyan 7.

Tsohon gwamnan jihar Abia  Najeriya,Orji Uzor Kalu
Tsohon gwamnan jihar Abia Najeriya,Orji Uzor Kalu Solacebase
Talla

Alkalin kotun Mohammed Idris ya bayyana hukuncin yau bayan samun sa da laifi dangane da tuhumar da ake masa tare da kamfaninsa na Slok Nigeria Limited da kuma daraktan kula da kudade a fadar gwamnatin jihar Abia Udeh Udeogu lokacin da ya mulki jihar.

Mr Kalu da kamfanin sa, Slok Nigeria Limited, da Udeh Udeogu, wanda shine darakta mai kula da kudade a yayin mulkin Kalu na shekaru 8 sune suka fuskanci kuliya.

A cikin jerin tuhume – tuhume har guda 39, ana zargin su ne da laifin karkata akalar sama da naira biliyan 7 daga asusun gwamnatin jihar.

A daya daga cikin tuhume – tuhumen da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Najeriya gabatar, ta zargi Uzor Kalu wanda ya yi mulkin jihar Abia daga shekarar 1999 zuwa 2007 da sayen kamfanin Slok Nigeria Limited da kudin da ya zarce biliyan 7 na naira, kudaden da ake zargin ya sake musu muhalli.

Yayin sauraron karar, masu gabatar da karar sun kawo shaidu 19, yayin da masu kare kansu suka yi shaidan kansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.