Isa ga babban shafi
Libya-Turai

Jakadun Turai sun bukaci sakin 'yar majalisar Libya da aka sace

Jakadun Kasashen Turai 13 cikinsu harda na kungiyar kasashen Turai EU, sun bukaci gudanar da binciken gaggawa kan bacewar wata ‘yar majalisar dokokin Libya domin ganin an sake ta.

Seham Sergewa, ‘yar majalisar Libya da ‘yan bindiga suka sace a birnin Benghazi.
Seham Sergewa, ‘yar majalisar Libya da ‘yan bindiga suka sace a birnin Benghazi. Middle East Monitor
Talla

Sanarwar da jakadun suka sanyawa hannu ta bayyana damuwarsu kan bacewar Siham Sergewa, tun a ranar 17 ga watan Yuli, bayan an kai mata hari gidanta dake Benghazi.

Cikin Jakadun da suka sanya hannu sun hada da na kungiyar kasashen Turai da na kasashen Austria da Belgium da Bulgaria da Finland da Faransa da Jamus da Italia da Holland da Portugal da Spain da Sweden da kuma Birtaniya.

Gungun ‘yan bindiga sun sace Siham Sergewa ne, bayan jikkata mijinta, jim kadan bayan zantawar ‘yar majalisar da kafar talabijin ta Al-Hadath dake goyon bayan Janar Khalifa Haftar, mai iko da gabashin kasar Libya.

Yayin tattaunawar, yar majalisar da tayi fice wajen sukar dakarun Haftar, ta bukaci gaggauta kawo karshen zubar da jinin ‘yan kasar, da tace yunkurin Janar Haftar na kifar da gwamnatin Libya da kasashen duniya ke marawa baya ya haddasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.