Isa ga babban shafi
Libya

An cimma yarjejeniyar tsagaitar wutar yakin Libya

Dakaru masu biyayya ga Janar Khalifa Haftar na Libya sun amince da yarjejeniyar tsagaita wutar yakin da suke gwabzawa da sojin gwamnati da Majalisar Dinkin Duniya ke goyon baya domin samun sararin gudanar da bukukuwan Sallar layya.

Wasu daga cikin dakarun Janar Khalifa Haftar na Libya.
Wasu daga cikin dakarun Janar Khalifa Haftar na Libya. REUTERS/Stringer
Talla

Gwamnatin ta Libya da ke Tripoli ce ta soma amincewa da yarjejeniyar tsagaita wutar, karkashin sulhun wucin gadin da majalisar dinkin duniya ta jagoranta.

Tun a farkon watan Afrilun da ya gabata, dakarun Khalifa Haftar ke gumurzu, da zummar karbe Tripoli daga hannun gwamnatin hadaka ta Libya.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce sabon fadan na Libya da ya barke, ya halaka mutane dubu 1 da 93, wasu dubu 5 da 752 sun jikkata, yayinda wasu dubu 120 kuma suka tsere daga muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.