Isa ga babban shafi

Harin ta'addanci ya kassara sashen yawon bude ido a Burkina Faso

Hare haren Yan ta’adda sun tilastawa baki daga kasashen Turai dake zuwa Yawon bude ido Burkina faso kauracewar kasar, abinda yayi sanadiyar asarar irin kudaden da kasar ke samu.

Jami'an tsaron Burkina Faso bayan harin da ya hallaka fararen hula 4 a kasar
Jami'an tsaron Burkina Faso bayan harin da ya hallaka fararen hula 4 a kasar AFP/Getty Images
Talla

Gwamnan Hauts-Basssin, Antoine Atiou ya ce tashin hankalin da kasar ke fama da shi, ya sa baki sun daina ziyarar da suke, matsalar da ta shafi harkokin kasuwanci da otel otel.

Rahotanni sun ce akalla mutane 600 aka kashe sakamakon tashin hankalin da ke gudana a kasar a cikin shekaru 4 da suka gabata, cikin su harda 'Yan kasashen waje.

A baya bayan nan ne, hare hare ke ci gaba da tsananta a kasar ta Burkina Faso ciki har da na kungiyoyi masu ikirarin jihadi da kuma 'yan bindiga dadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.