Isa ga babban shafi
Najeriya

Jami'an tsaro sun mamaye wajen zanga-zangar RevolutionNow

Jami’an tsaro a Najeriya sun mamaye harabar wuraren da ake sa ran zanga-zangar kin jinin gwamnati a kasar da aka yiwa lakabi da RovolutionNow, zanga-zangar da gwamnatin kasar ke zargin wasu tsirarun ‘yan adawa da kitsawa da nufin kara tarnaki ga kasar wadda ke fuskantar matsalolin tsaro.

Wasu jami'an tsaro na Musamman a Najeriya
Wasu jami'an tsaro na Musamman a Najeriya AFP PHOTO / Quentin Leboucher
Talla

Rahotanni sun bayyana cewa a jihar Lagos, jami’an tsaro na musamman sun mamaye babban filin wasanni da ke Surulere.

A cewar wata Majiya daga jihar ta Lagos jami’an tsaron da aka jibge ba nau’in wadanda aka saba gani ba ne don bayar da tsaro a wuraren zanga-zanga, a cewar majiyar jami’ai ne na hadaka da suka kunshi Sojin Sama na ruwa da kuma na kasa dukkanninsu dauke da makamai.

Tun a ranar Asabar din da ta gabata Rundunar 'yan sandan Najeriyar ta gargadi masu zanga-zangar ta RevolutionNow tare da barazanar ayyana duk wanda ya shiga gangamin a matsayin dan ta'adda, baya ga daukar matakin kame jagoran zanga-zangar a daren Juma'a.

Mawallafin ‘Sahara Reporters’ Omoyele Sowore ne dai tare da wasu masu fafutukar kare hakkin jama’a suka kira gangamin a fadin Najeriya, domin nuna rashin amincewa da yadda talauci da rashin tsaro da kuma kuncin rayuwa suka yiwa al’ummar kasar dabaibayi.

Gwamnatin Najeriya ta bukaci jama’a da su kara hakuri saboda kokarin da take na shawo kan matsalolin da suka addabi kasar, amma masu shirya zanga zangar sun bukaci jama’a da su yi watsi da bukatar wajen fitowa domin nuna fushin su akai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.