Isa ga babban shafi
Afrika

An gudanar da Jana'izar marigayi shugaba Essebsi na Tunisia

Dubun dubatar al’ummar Tunisia yau Asabar sun halarci jana’izar shugaba Beji Caid Essebsi da ya koma ga mahaliccinsa ranar Alhamis din da ta gabata, bayan fama da rashin lafiya.Shugaban wanda ya jagoranci kasar bayan fuskantar juyin-juya halin 2011, ya rasu yana da shekaru 92 a duniya, kuma ya na matsayin shugaba mafi tsufa a duniya.

Jana’izar Shugaban Tunisia Muhammad Essebsi
Jana’izar Shugaban Tunisia Muhammad Essebsi Fethi Belaid / AFP / POOL
Talla

Baya ga wakilan kasashen duniya daban-daban da suka halarci taron Jana'izar akwai kuma sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani baya ga shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron.

Sauran shugabannin da suka halarci Jana'izar marigayi shugaba Essebsi da ta gudana a Tunis babban birnin kasar ta Tunisia sun hada da takwaransa na Algeria Abdelkader Ben Saleh, da shugaban Falsdinawa Mahmoud Abbas sai sarkin Spain Felipe na VI.

Yayin jana'izar an kulle manyan titunan da za su sada al'umma da babban birnin yayinda 'yan kasar suka katse zirga-zirga don nuna alhini da jimamin rabuwa da shugaban.

Bayan kammala jana'izar tsohon shugaban na Tunisia Beji Caid Essebsi, wanda cikakken sunansa shi ne Mohamed Caid Essebsi, an binne shi bisa tanadin addinin Islama tare da gudanar da addu'o'i.

An dai haifi Muhammad Essebsi ranar 29 ga watan Nuwamban 1926 a yankin Sidi Bou Said kuma shi ne shugaban kasar Tunisa na 5 haka zalika zababben shugaba na farko a tarihin kasar.

Shugaban wanda ya rike mukamin ministan harkokin wajen kasar a shekarar 1981 har zuwa 1986 shi ne Firaminista tun daga watan Fabarairun 2011 har zuwa Disamba kafin karbar ragamar shugabancin kasar a shekarar 2014.

Mohamed Caid wanda jika ne wajen Ismail Caid Essebsi da ya mulki kasar tun a karni na 19, ya fara harkokin siyasa ne tun ya na da karancin shekaru a duniya, kuma ya na da yara 4 da suka kunshi mata 2 da maza guda 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.