Isa ga babban shafi
Kamaru

Kamaru ta gurfanar da Sojinta 7 kan kisan mata 2 a arewacin kasar

Ma'aikatar tsaron kasar Kamaru ta ce za a fara sauraron shari'ar sojin kasar 7 da ta  gurfanar a gaban kotu don fuskantar hukuncin bayan samunsu da laifin kisan wasu mata 2 a yankin arewacin kasar mai fama da rikici.

Wasu dakarun sojin kasar Kamaru.
Wasu dakarun sojin kasar Kamaru. REUTERS/Joe Penney
Talla

Sanarwar da ofishin Ministan tsaron kasar ta Kamaru ta fitar ta bayyana cewa tuni ma'aikatar tsaron kasar ta mika batun gaban kotun Soji da ke birnin Yaounde don fara yiwa sojojin hukunci dai dai da laifinsu.

Rahotanni sun bayyana cewa a watan Yulin 2018 ne sojojin 7 suka hadu wajen kisan matan biyu da 'ya'yansu a yankin arewacin kasar mai fama da rikici wanda kuma bayan tafka aika-aikar ne bidiyon kisan ya yadu a shafukan sada zumunta.

Ko da dai sanarwar ministan tsaron na Kamaru ba ta fayyace ranar da za a fara shari'ar sojin ba, amma ta tabbatar da cewa bincikenta ya nuna ta'asar da sojin suka aikata wanda kuma ke bukatar hukuncin din biwa matan hakkinsu.

Sanarwar ta bayyana cewa har kullum kasar Kamaru za ta ci gaba da mutunta dokokin kare hakkin bil adam baya ga daukar matakan kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

A baya dai hukumomin Kamaru sun musanta zargin bayan bayyanar bidiyon a kafofin sada zumunta, kafin daga bisani gwamnatin ta amince bayan tsananta bincike.

Da jimawa kungiyoyi masu zaman kansu na zargin dakarun Kamaru da kaucewa dokokin kare hakokin bil Adam tareda yin amfani da karfi da ya wucce kima zuwa farraren fula a yankunan arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.