Isa ga babban shafi
Sudan

Sojoji sun bude wuta kan masu zanga-zanga a Sudan

Rahotanni daga Sudan sun je an jiwo rugugin tashin bindigogi a Khartoum, yayinda sojoji sukai amfani da karfi, wajen tarwatsa sansanin da masu zanga-zanga suka kafa babban birnin kasar.

Dubban masu zanga-zanga a hedikwatar rundunar sojin kasar Sudan da ke birnin Khartoum.
Dubban masu zanga-zanga a hedikwatar rundunar sojin kasar Sudan da ke birnin Khartoum. AFP/Getty Images
Talla

Kwamitin likitocin Sudan ya ce mutane 2 sun rasa ransu, yayin da kuma wasu da dama suka jikkata, bayan da sojojin suka bude wuta kan gungun masu zanga-zanga da ke ci gaba da zaman dirshan a birnin Khartoum.

Tun bayan da a watan Afrilu, sojin Sudan suka kawo karshen mulkin kusan shekaru 30 na tsohon shugaban kasar Omar Al Bashir, har yanzu masu-zanga-zanga na ci gaba da zaman dirshan a gaban hedikwatar rundunar sojin kasar ta Sudan, da nufin tilasta musu mika mulki ga gwamnatin farar hula.

A karshen makon da ya gabata, sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterresh, ya bukaci sojin kasar Sudan da jagororin masu zanga-zanga, su ci gaba da tattaunawar da suke yi kan cimma yarjejeniyar mika mulki ga farar hula, wadda suka dakatar.

A ranar 14 ga watan Mayu, bangarorin 2 suka cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa tsakanin farar hula da soji, wadda bayan shekaru 3 za ta mika mulkin ga cikakkiyar gwamnatin farar hula.

Yarjejeniyar ta kuma amince da kafa majalisa mai mambobi 300, kuma kashi 2 bisa 3 na ‘ya’yanta za su fito ne daga bangaren kawancen masu zanga-zangar.

Daga bisani ne tattaunawar ta dakata, bayan da sojojin suka bukaci masu zanga-zanga su cire shingayen da suka kafa. Ranar 19 ga watan Mayu kuma bangarorin suka sake komawa teburin shawara, amma aka rabu baran-baran, saboda gaza cimma matsaya kan wanda ya dace ya shugabanci gwamnatin hadakar da za a kafa, walau daga bangaren sojin ko kuma na farar hular.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.