Isa ga babban shafi
Sudan

Sudan: Masu zanga-zanga sun nemi mika manyan mukamai ga fararen hula

Jagororin masu zanga-zanga a Sudan sun ce za su mika bukatar bai wa fararen hula damar jagorancin sabuwar gwamnatin hadakar da za a kafa a kasar yayin komawarsu teburin tattaunawa da bangaren soji yau Lahadi, dai dai lokacin da wasu jagororin masu faftukar addinin Islama ke fatan ganin an sanya dokokin addini a tafiyar sabuwar gwamnatin.

Dubban masu zanga-zanga a kofar shalkwatar sojin kasar Sudan
Dubban masu zanga-zanga a kofar shalkwatar sojin kasar Sudan Photo: AFP
Talla

Sanarwar da hadakar jagororin masu zanga-zangar ta masu fafutukar samar da ‘yanci tare da sauyi a kasar ta fitar, ta nuna cewa akwai bukatar jagoran sabuwar gwamnatin ya kasance farar hula yayinda za a baiwa soji damar ta cewa a mulkin kasar.

Sanarwar hadin gwiwar tsakanin bangarorin jagororin masu zanga-zangar ta nuna cewa da misalin karfe 9 na daren yau ne za su ci gaba da tattaunawa da bangaren sojin wadanda ke ci gaba da mulkin kasar tun bayan hambarar da shugaba Omar al-Bashir daga mulki a ranar 11 ga watan Aprilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.