Isa ga babban shafi
Mozambique

An samu barkewar Kwalera a Mozambique

Jami’an Lafiya a Mozambique, sun bada tabbacin bullar cutar kwalara a yankunan kasar da Iftila’in Guguwa da Ambaliyar ruwa ya afkawa a makon da ya gabata.

Jami'an Kiwon Lafiya sun yi gargadin cewa, cutar ta Kwalera za ta tsananta muddin aka yi sakacin magance ta cikin hanzari
Jami'an Kiwon Lafiya sun yi gargadin cewa, cutar ta Kwalera za ta tsananta muddin aka yi sakacin magance ta cikin hanzari © REUTERS
Talla

Kungiyar bada agajin gaggawa ta Red Cross ta dade tana gargadin yiwuwar bullar cutar a dalilin rashin kyawun muhalli da ruwan sha mai tsafta.

A ranar 15 ga watan Maris da muke ciki guguwar Idai ta afkawa Mozambique da Zimbabwe da Malawi dauke da ruwan sama mai karfin gaske, lamarin da ya haifar da gagarumar ambaliya da ta hallaka sama da mutane 700 a kasashen, baya ga wasu sama da dubu 500 da ta raba da muhallansu.

Tuni dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta bada umarnin aikewa da magungunan rigakafin cutar ta kwalara akalla dubu 900 kafin ta kai ga girmama zuwa annoba, a tsakanin mutane miliyan 3 da iftila’in ambaliyar ya shafa a kasashen na Mozambique da  Zimbabawe da kuma Malawi.

Jami’an lafiya a kasar ta Mozambique sun ce, yanzu haka suna lura da marasa lafiya akalla dubu 2 da 700 da suka nuna alamun kamuwa da cutar ta Kwalara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.