Isa ga babban shafi
Najeriya

Yan Sanda sun cafke Buba Galadima

Rahotanni daga Najeriya na nuni cewa jami’an tsaro sun cafke na hannun daman dan takarar Shugabancin kasar na babbar jam’iyyar adawa ta PDP Buba Galadima, kamar yadda shugabancin jam’iyyar ya tabbatar.

Engr Buba Galadima na hannun damar dan takarar jam'iyyar PDP
Engr Buba Galadima na hannun damar dan takarar jam'iyyar PDP News Dairy
Talla

Kawo yanzu babbu karin bayyani dangane da dalilin kama shi da aka yi, sai kakkakin jam’iyyar ta PDP Kola

Ologbonyan, ya ce an kama shi ne a Abuja.

Matakin ya zo ne awanni kadan bayan da kakakin yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari, Festus Keyamo ya bukaci da a kama Buba Galadima, wanda ya ce ya fitar da wani bidiyo, da a cikinsa ya ke bayyana cewa Atiku Abubakar shi ne ya lashe zaben shugabancin Najeriya, duk da cewa hukumar zaben kasar INEC ba ta kai ga bayyana sakamakon zaben ba.

‘Yan takara 73 ke fafatawa a matakin zaben kujerar shugaban Najeriyar, amma takarar ta fi zafi tsakanin shugaba mai ci Muhd Buhari da kuma dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.