Tattaunar gwamnati da 'yan tawaye ta gamu da cikas
Tattaunawar zaman lafiyar da ake gudanarwa a birnin Khartoum na Sudan tsakanin wakilan gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Yan Tawayen kasar, ta gamu da cikas, sakamakon bukatar afuwa ga daukacin ‘yan tawayen da aka gabatar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sabuwar tattaunawar da aka fara makon jiya wadda ta samu halartar wakilan gwamnati da shugabannin yan adawar, na zuwa ne bayan wasu yunkuri sau 7 da aka yi ba tare da an samu nasara ba.
Tun ranar Litinin tattaunawar ta mayar da hankali ne kan bukatun kungiyoyin guda 14, da suka fi karkata kan kafa gwamnatin hadin kai da kuma yiwa shugabannin su afuwa.
Sai dai gwamnatin Afrika ta Tsakiyan taki amincewa da bukatun.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu