Isa ga babban shafi
Cote D'Ivoire

Sallamar Gbagbo ko ci gaba da tsare shi?

Wani lokaci a yau juma'a ake sa ran kotun Duniya da ke birnin Hague za ta sallami tsohon shugaban Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo da kuma wani na hannun damansa Charles Ble Goude, duk da cewa bangaren masu shigar da kara sun nuna rashin amincewarsu da matakin.

Laurent Gbagbo da Charles Blé Goudé a kotun  Duniya
Laurent Gbagbo da Charles Blé Goudé a kotun Duniya AFP-Photo/Montage RFI
Talla

A ranar Alhamis 28 ga watan janairu 2016 ne aka soma zaman shari’ar tsohon Shugaban Cote D’Ivoire Laurent Gbagbo a kotun ICC da ke hukunta laifukan yaki ta duniya da ke birnin Hague. Ana zargi Gbagbo da tayar da rikiciin da ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane dubu uku a lokacin rikicin zaben kasar na shekara ta 2010.

Gbagbo ya kasance shugaban kasa na farko da ya gurfana gaban kotun ICC, inda wasu mutanen Afrika ke zargin Kotun da farautar shugabannin Afrika kawai.

Tun kafa ta a 2002 domin hukunta laifukan yaki, kotun ta mayar da hankali a Afrika kamar yadda ta kaddamar da bincike a kasashen Sudan da Libya da Uganda da Mali da Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da Cote d’Ivoire da Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo.

Amma da dadewa Kotun na kare kanta inda Babbar mai gabatar da kara a kotun Fatou Bensouda ‘yar kasar Gambia a Nahiyar Afrika ke cewa da bukatun kasashen ne kotun ke aiki.

Baya ga Gbagbo, akwai Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir da Kotun ICC ta bayar da sammacin kamo shi kan rikicin Darfur.

Kowane lokaci a yau kotun za ta iya bayyana matsayinta na amincewa ko kuma kin amincewa da sakin mutanen biyu da ake zargi da tayar da rikicin da ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane dubu 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.