Isa ga babban shafi
Najeriya-Kwastam

Kwastam ta raba buhunan shinkafar da ta kwace ga 'Yan gudun hijira

Hukumar da ke yaki da Fasakwaurin kayaki a Najeriya Kwastam ta raba buhunan shinkafa dubu dari hudu da 23 da dari 3 da 91 ga ‘yan gudun hijirar da rikici ya raba da muhallansu a jihohin Borno Yobe Adamawa da kuma jihar Edo.

Kwastam ta kwace akalla buhunan shinkafa masu nauyin kilogiram 50 dubu 238 da 094 tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamban shekarar nan.
Kwastam ta kwace akalla buhunan shinkafa masu nauyin kilogiram 50 dubu 238 da 094 tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamban shekarar nan. The Guardian Nigeria
Talla

Kakakin Ofishin mataimakin kwanturolan hukumar ta Kwastam Joseph Attah, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriyar cewa, kiyasin kudin shinkafar ya haura Naira biliyan 4.

A cewarsa matakin ya biyo bayan umarnin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi na rabawa ‘Yan gudun hijrar tarin Shinkafar da hukumar ta kwace daga hannun masu safararta daga ketare bayan hanin da gwamnati ta yi.

Kakakin hukumar ta Kwastam ya kuma bayyana cewa, baya ga shinkafar akwai kuma tarin haramtattun kayayyaki da Najeriyar ta hana shigo mata da su, wadanda suma hukumar ta kwace inda za ta rarrabasu ga ‘yan gudun hijirar.

Rahotanni na nuni da cewa hukumar ta Kwastam ta kwace akalla buhunan shinkafa masu nauyin kilogiram 50 dubu 238 da 094 tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamban shekarar nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.