Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan sanda 12 sun jikkata yayin artabu da 'yan bindiga

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta hallaka adadi mai yawa na ‘yan bindiga da ya kai 104, tare da tarwatsa sansanoninsu sama da 40, a kazamin artabun da suka yi a dajin Mahanga dake Zamfara a arewacin kasar, bayan kaddamar da samamen kawo karshen hare-hare da satar jama’a a jihar.

Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya.
Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya. TheTrentOnline
Talla

A cewar rundunar yayin jerin sumamen da ta kai dazukan jihar ta Zamfara a baya-bayan nan ta lalata maboyar ‘yan bindigar fiye da 50 baya ga gano shanu sama da 500 da tumaki 79.

Cikin sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Jimoh Moshood,  ya ce farmakin rundunar ya gudana ne a ranar Alhamis 29 ga watan Nuwamba, kuma sun samu nasarar kwace bindigogi kirar AK47 27 da wasu kirar gida 52.

Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa, 'yan bindigar sun jikkata jami'ansu 12 tare da hallaka 1, yayin artabun da suka fafata.

A farkon watan Nuwamba rundunar 'yan sandan Najeriya ta aika da karin jami’anta sama da dubu daya jihar ta Zamfara, kuma daga lokacin zuwa yanzu, sun yi nasarar damke akalla mutane 85, wadanda ake zargin suna da hannu wajen aikata laifukan sacewa da yin garkuwa da mutane, da kuma satar dabbobi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.