Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnonin Najeriya sun amince da samar da 'Yansandan jihohi

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta nuna goyon baya ga bukatar mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo na samar da ‘yansandan jihohi don bayar da cikakkiyar kariya ga al’umma a kananan matakai.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari lokacin da yake jawabi kan amincewarsu da samar da 'Yansandan jihohi.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari lokacin da yake jawabi kan amincewarsu da samar da 'Yansandan jihohi. NAN
Talla

Kungiyar karkashin jagorancin gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ta ce matakin abin maraba ne la’akari da barazanar tsaron da Najeriyar ke fuskanta a baya-bayan.

Da ya ke jawabi ga manema labarai bayan kammala wani taron kwanaki biyu kan matakan tsaron da ya kamata a kara dauka a Najeriyar wanda majalisar dattijan kasar ta shirya, Abdul’aziz Yari wanda Jiharsa na daga cikin yankunan kasar da rashin tsaro ya tsananta, ya ce kungiyar ta amince da samar da hukumar ‘yansandan karkashin ikon jihohi.

Ko da ya ke dai Yari ya ce babban kalubale ga jihohin kasar shi ne yadda za a samar da kudaden daukar nauyin hukumar.

Abdulaziz Yari ya ce za a fara aikin samar da ‘yan Sandan jihohin ne a rukuni rukuni kafin daga bisani a fadada shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.