Isa ga babban shafi
Najeriya-Zabe

Kasashen duniya sun bukaci gudanar da sahihin zabe a Najeriya

Kungiyar Tarayyar Turai da Amurka da Birtaniya da Faransa sun bukaci ganin an gudanar da karbabben zabe a Najeriya wanda duniya za ta amince da shi.Wannan bukata ta fito daga wadannan kasashe sakamakon kaddamar da yakin neman zaben shekara mai zuwa da aka fara yau lahadi, kamar yadda hukumar zabe ta tanada.

Sanarwar ta ce bukatar su ita ce ganin an gudanar da karbaben zabe da Yan Najeriya da kuma kasashen duniya za su yaba da shi.
Sanarwar ta ce bukatar su ita ce ganin an gudanar da karbaben zabe da Yan Najeriya da kuma kasashen duniya za su yaba da shi. AFP/Pius Utomi Ekpei
Talla

Sanarwar da kungiyar kasashen Turai da Amurka da Birtaniya da Faransa suka sanyawa hannu ta bukaci shirya zaben da kuma gudanar da shi cikin yanayi mai kyau da kwanciyar hankali da kuma kaucewa duk wata matsalar da za ta iya tayar da hankalin jama’a.

Kasashen da suka sanya hannu kan sanarwar sun bayyana cewar, a matsayin su na kawayen Najeriya da kuma mutanen ta, zasu bi sau da kafa yadda za a gudanar da yakin neman zaben da kuma zaben kan sa domin sa ido akai.

Sanarwar ta ce bukatar su ita ce ganin an gudanar da karbaben zabe da Yan Najeriya da kuma kasashen duniya za su yaba da shi.

Kasashen sun kuma bukaci ganin mata da matasa sun shiga harkokin zaben a matakai daban daban an dama da su, tare da wadanda ke fama da nakasa a jikin su.

Kasashen sun bukaci Yan siyasa da su kaucewa kalamun batunci da ke tayar da hankali, tare kuma da bai wa hukumar zaben yancin gudanar da ayyukan ta ba tare da samun katsalandan ba.

Sauran kasashen da suka sanya hannu kan sanarwar sun hada da Italy da Spain da Sweden da Netherlands da Norway da Portugal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.