Isa ga babban shafi
Senegal

Kotun Senegal ta goyi bayan daure Khalifa Sall

Wata kotun Senegal ta goyi bayan hukuncin daurin shekaru biyar kan fitaccen dan siyasar kasar Khalifa Sall, abin da ya haramta masa tsayawa takara a zaben shugaban kasa da za a gudanar a cikin watan Fabairun badi.

Fitaccen dan siyasar Senegal  Khalifa Ababacar Sall
Fitaccen dan siyasar Senegal Khalifa Ababacar Sall AFP/SEYLLOU
Talla

Khalifa Sall mai shekaru 62 kuma magajin garin Dakar, ya bayyana hukuncin kotun da tasirin siyasa duk da cewa bai samu damar halartar zaman kotun ba a yau Alhamis.

A cikin watan Maris da ya gabata ne aka yanke masa hukuncin dauri bayan an tuhume shi kan barnatar da dukiyar talakawa, yayin da aka ci tarar sa Euro dubu 7 da 625, kwatankwacin CFA biliyan 1.8.

Koda yake kotun ba ta samu dan siyasar da aikata manyan laifukan da suka shafi cin amanan kasa da wawure dukiya ba.

Shari’ar Sall ta dauki hankula matuka, in da tun a farkon wannan shekarar al’ummar kasar suka fara bibiyar ta sau-da-kafa, abin da ya jefa shakku kan makomar farin jinin dan siyasar, yayin da ake tafka muhawa kan wanda zai gaji kujerar shugabancin kasar bayan haramta masa tsayawa takara.

Sai dai wata kwakkwarar majiya ta ce, Sall zai daukaka kara a kotun koli a wani yunkuri na ganin ya samu damar shiga fagen gwagwarmayar neman kujerar shugaban kasa a badi.

Ana kallon Sall a matsayin babbar barazana ga shugaban kasar mai ci, Macky Sall da babu wata dangantakar jini da ta hada su duk da cewa, suna amsa Sall a sunayensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.