Isa ga babban shafi
Kamaru

Hukumar zaben Kamaru ta tsayar da yan takara 9 a zaben shugabancin kasar

Yan takara 9 da suka hada da shugaban kasar mai barin gado Paul Biya, mai shekaru 85 a duniya da ya kwashe shekaru 35 kan mulki ne, hukumar zaben kasar Kamaru ta amince da takararsu a zaben shugabancin kasar da za a yi a ranar 7 ga watan October mai zuwa.

shugaban kasar Kamaru Paul Biya a zauren taron Majalisar Dinkin Duniya  karo na 71 22 septembre 2016.
shugaban kasar Kamaru Paul Biya a zauren taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 71 22 septembre 2016. REUTERS/Mike Segar
Talla

Baya ga shugaba Biya na jam’iyar (RDPC), manyan yan adawar da aka tabbatar da sahihancin takarsu, sun hada ne da Joshua Osih, na (SDF), babbar jam’iyar adawar kasar, sai Garga Haman Adji, na jami’iyar (ADD), da ya zo na uku a zaben shugabancin kasar da ya gabata na 2011.

Har ila yau, a kwai wasu yan takara jam’iyun adawa, da suka hada da lauyan nan dan asalin yankin dake amfani da turancin inglishi Akere Muna, da jam’iyar (FPD) ta tsayar, sai Maurice Kamto na jam’iyar (MRC), da Cabral Libii na jam’iyar Univers.

Bugu da kari, yan takarar sun hada da Adamou Dam Njoya, na jam’iyar (UDC), Serge Espoir Matomba, na jam’iyar (Purs) da Frankline Ndifor Afanwi, jam’iyar (Mcnc).

A jimilce dai, hukumar zaben kasar ta Kamaru, Elecam, ta karbi takardun yan takara 28 ne, inda ta yi watsi da 18, da ta ce basu cancanci tsayawa takara ba.

Bayan fitar da sunayen yan takarar dai, dan adawa Cabral Libii, da aka sani sosai, sakamakon yawan bayyanarsa a kafafen yada labarai da kuma shafukan sadarwar al’umma na Internet, ya yi kiran sauran yan takarar hadin guiwar jam’iyun adawa da cewa, su tsaida dan takara guda, da za su mara wa baya domin kalubalantar shugaba Paul Biya da ya share shekaru 35 yana kankame da kujerar shugabancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.