Isa ga babban shafi
Afrika

Shugabannin Afrika na tattauna batun tsaro a taronsu

Taron Kungiyar Kasashen Afrika da ke gudana a birnin Nouakchott na Mauritania zai bada muhimmanci kan matsalar tsaro wadda ke ci gaba da tabarbarewa, yayin da a baya-bayan nan aka kai sabon farmaki kan sojojin Faransa a Mali.

Zauren taron shugabannin kasashen Afrika a birnin Nouakchott na Mauritania
Zauren taron shugabannin kasashen Afrika a birnin Nouakchott na Mauritania Ahmed OULD MOHAMED OULD ELHADJ / AFP
Talla

Harin bama-baman da aka kai kan dakarun na Faransa da ke aikin sintiri a yankin arewacin Mali mai fama da tashin hankali, ya hallaka fararen hula akalla hudu tare da raunata mutane 20 da suka hada da sojoji hudu.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, aka kai harin kunar bakin wake kan shalkwatan rundunar tsaro ta kasashen G5 Sahel a Mali, lamarin da ke kara nuna yadda matsalar tsaron ke ci gaba da tabarbarewa.

A karon farko kenan da 'yan ta'adda suka dirar wa shalkwatan wanda Faransa ta taimaka wajen kafawa a shekarar 2017 don yaki da ‘yan ta’addan da ke tayar da kayar-baya a yankin Sahel.

Shugabannin Kasashen Yankin Sahel da suka hada da Mali da Burkina Faso da Mauritania da Nijar da kuma Chadi sun gana da juna a ranar Lahadi a gefen taron na Kungiyar Kasashen Afrika kamar yadda wata ma jiyar diflomasiya ta tabbatar.

Majiyar ta ce, shugabannin na yankin Sahel sun yi ganawarce don kintsa wa ganawar da za su yi da shugaban Faransa Emmanuel Macron da ake dakon isarsa taron a ranar Litinin.

Fiye da shugabannin kasashen Afrika 40 ne ke halartar taron na bana a  Mauritania, in da kuma za su zanta kan matsalar cin hanci da rashawa da kasuwancin bai-daya baya ga batun tsaro da zai mamaye taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.