Isa ga babban shafi
Afrika ta tsakiya

Kotun hukunta laifufukan yaki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta kafa kotun musamman domin bincike tare da hukunta wadanda ake zargi da aikata laifufukan yaki daga shekara ta 2003 zuwa yau a kasar.

Antonio Guterres, Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya na ziyarar a birnin Bangui
Antonio Guterres, Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya na ziyarar a birnin Bangui RFI/Pierre Pinto
Talla

An share tsawon shekaru uku ana fatan kafa wannan kotu amma sai zuwa a jiya talata ne majalisar dokokin kasar ta amince da hakan da gagarumin rinjaye.

Da zarar shugaban kasa ya sanya wa dokar hannu, nan take mai shigar da kara na kotun wanda dan asalin kasar Congo ne da kuma mukarrabansa, za su fara aikin bincike don gurfanar da wadanda ake tuhuma.

Ana zargin bangarori da ke da hannu a yake-yaken basasar da suka faru a kasar da hannu wajen kisa da kuma gallaza wa jama’a.

Yayin da Flavien Mbata ministan shara’a ke cewa kotun za ta hukunta duk wadanda aka sama da laifi, shi kuwa Florent Kema, dan majalisar dokoki daga bangaren adawa, na ganin cewa yanayin rashin tsaro da ake fama da shi a kasar ba zai bai wa kotun damar gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyanta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.