Isa ga babban shafi
Burundi

'Yan bindiga sun hallaka mutane 26 a Burundi

Akalla Mutane 26 suka mutu, yayin da 7 suka jikkata sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai suka kai a kauyen Buganda dake arewa maso mammacin Burundi.

Wani jami'in tsaron kasar Burundi.
Wani jami'in tsaron kasar Burundi. AFP
Talla

Bayanai sun ce maharan sun shiga Burundi ne daga Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo bayan sun tsallake kogin Rusizi da kwale kwale.

Jami’in da ke kula da yankin na Buganda Emmanuel Bigirimana ya ce maharan sun bude wuta kan mai uwa da wabi, kuma cikin wadanda harin ya ritsa da su harda dattijai da yara.

Daga bisani maharan sun tsere zuwa Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo ba tare da sun dauki komai ba, sai dai kisan rayukan da suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.