Isa ga babban shafi
Madagascar

Shugaban Madagascar ya soke dokar haramtawa 'yan adawa takara

Shugaban kasar Madagascar Hery Rajaonarimpianina, ya amince da wata sabuwar dokar zaben kasar, da ta dage haramcin da a baya ya hau kan madugun ‘yan adawa kuma tsohon shugaban kasar Marc Ravalomanana na sake tsayawa takara.

Madugun 'yan adawa kuma hambararren shugaban kasar Madagascar Marc Ravalomanana yayin jawabi a wani taro a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu.
Madugun 'yan adawa kuma hambararren shugaban kasar Madagascar Marc Ravalomanana yayin jawabi a wani taro a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu. REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Matakin na shugaba Rajao-narimam-pianina, ya biyo bayan hukuncin kotun kolin kasar da ya bayyana dokar ta baya a matsayin haramtacciya.

Dokar da ta haramtawa ‘yan adawa ciki har da tsohon shugaba Ravalo-manana tsayawa takarar shugabancin kasar ta haddasa kazamar zanga-zanga a sassan kasar ta Madagascar, abinda ya sa tilas kungiyar trayyar Afrika ta sanya baki cikin rikcin siyasar kasar.

Marc Ravalomanana, ya shugabanci Madagascar daga shekarar 2002, zuwa 2009, lokacin da aka yi masa juyin mulki.

Bayan zarginsa da aikata ba dai dai ba ciki harda cin hanci da rashawa a lokacin da yake gudun hijira, gwamnatin kasar ta kakabawa Ravalomanana haramcin sake neman shugabancin kasar.

Magadascar na daga cikin kasashe mafi fama da talauci a duniya, duk da arzikin ma’adanan Nickel, Zinare, da kuma Uranium da kasar ke da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.