Mali
Yan bindiga sun kashe dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Kidal
Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe dakarun ta guda biyu dake aikin samar da zaman lafiya a Mali, yayin da aka raunana wasu guda 10 a harin da aka kai sansanin su dake Aguelhok.
Wallafawa ranar:
Talla
Kungiyar MINUSMA dake kula da dakarun, ta ce an kai harin ne da misalin karfe 6 da mituna45 na yammacin jiya juma’a, lokacin da aka harba musu makami mai linzami.
Ya zuwa yanzu ba’a iya tantance ko sojojin wacce kasa ne hadari ya ritsa da su ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu