Isa ga babban shafi
Chadi

Taron yiwa kundin tsarin mulkin Chadi garambawul

Bayan tafka muhawara tsakanin mahalarta taron yiwa kundin tsarin mulkin kasar Chadi garambawul na tsawon mako guda,mahalarta taron sun soma cimma matsaya kan manyan batutuwan da kwamitin shirya taron ya kayyade,duk da rashin kasancewar manyan jam'iyyun siyasar kasar a wannan zama.

Idriss Déby Itno, Shugaban kasar Chadi
Idriss Déby Itno, Shugaban kasar Chadi PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Ana kyautata zaton cewa wannan taro zai kayyade wa’adin shugabancin kasar a dai dai lokacin da shugaba mai ci Idris Deby ke share shekaru 27 kan madafun iko.

A jawabin da ya gabatar wurin bude wannan taro, shugaba Idris Deby wanda ke fuskantar suka daga bangaren 'yan adawan kasar, ya yi fatan taron zai haifar da sakamako nagari ga kasar.

Kungiyoyin fararen hula na zargin Shugaban Deby da karbar rashawa daga wasu kamfanonin kasashen waje, a lokacin da jama'a ke kokawa ganin halin rayuwar da suka samu kan su musamman kan abin da ya shafi rashin kulawa daga gwamnati.

Wakilinmu a kasar Chadi Tijjani Mustapha Mahadi ya aiko mana da rahoto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.