Isa ga babban shafi
Kamaru

An kashe Jandarma uku a yankin 'yan awaren Kamaru

Yan bindiga da ake zaton ‘yan aware ne sun kashe jami’an tsaron Jandarmomi uku, a kudu maso yammacin Kamaru, yankin da aka jibge jami’an tsaro domin sake dawo da zaman lafiya, tun bayan da 'yan awaren suka fara neman 'yancin kai.

Jami'an tsaron kasar Kamaru na sintiri a yankuna masu fama da rikici
Jami'an tsaron kasar Kamaru na sintiri a yankuna masu fama da rikici AFP
Talla

Kanal Didier Badjeck, kakakin rundunar tsaron kasar, a zantawar sa da manema labarai, ya ce “lamarin ya faru ne da safiyar  lahadi a kauyen Kembong, amma kuma tuni akayi nasaran kame maharan”.

A dan kwanakin nan ‘yan awaren na amfani da kafafen sada zumunta da muhawara na intanet, wajen yin barazanar kauracewa bukukuwan 11 ga watan fabraireru wato ranar da aka gudanar da zaben raba gardadama na shekara ta 1961, da ya hada ‘yankin renon Faransa da na Ingila, wanda daga bisani aka maida ranar ta koma ta matasa .

Larduna biyu,wato arewa maso yamma da kuma kudu maso yamma, na da kashi 20 cikin dari na al’umman kasar, da su ke ganin gwamnati na tirsasa musu, fiye da shekara yankin ya fada cikin rudanin siyasa da ma na zamantakewa wanda daga bisani ya rikide ya zama na kai hare-hare da makamai.

Ya zuwa yanzu rikicin ya haddasa mutuwar jami’an tsaro 26 tun bayan da 'yan awaren suka fara neman 'yancin kai, babu adadin ‘yan aware ko fararen hula da suka rasa rayukansu a hukumance.

A wani  dan karamin bincike daga kamfanin dilancin labaran Faransa  AFP an gano cewa ‘yan gudun hijira fiye da 33 000 suka baro gidajen su domin neman mafaka a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.