Gwamantin Kamaru ta karfafa matakan tsaro a Bamenda
Gwamnatin Kamaru ta kafa dokar hana fitar dare a Bamenba wanda shi ne babban birnin a yankin da ke amfani da Turancin Ingilishi a kasar.
Wallafawa ranar:
Wasu da ake zargin cewa ‘yan awaren yankin ne suka kashe jami’an tsaron kasar hudu a wannan mako.
Birnin zai ci gaba da kasancewa karkashin wannan doka har zuwa ranar 23 ga wannan wata tare da kafa wuraren binciken jama’a.
A baya dai ne Fira Ministan kasar Kamaru, Philemon Yang, ya kai ziyara tareda tuntubar juna a yankin Bamenda, dake arewa maso gabashjin kasar, a kokarin da gwamnatinsu ke yi na tattaunawa da mutanen yankin, dake amfani da turancin ingilishi a yankin, wanda a baya ya yi fama da rikice rikicen siyasa da na zamantakewa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu