Isa ga babban shafi
Libya

Harin masallacin Benghazi ya jikkata kusan mutane 100

Wasu hare-haren Bom da tsakar ranar yau a masallacin juma'a da ke birnin Benghazi na Libya ya hallaka mutum guda, yayinda ya jikkata kusan mutane 100.Rahotanni sun ce harin shi ne irinsa na farko a baya-bayan nan da aka kai wurin ibada.

Kawo yanzu dai babu kungiyar da ta dauki alhakin harin, yayin da ake ci gaba da baiwa mutanen da suka raunata kulawar gaggawa don ceto rayukansu.
Kawo yanzu dai babu kungiyar da ta dauki alhakin harin, yayin da ake ci gaba da baiwa mutanen da suka raunata kulawar gaggawa don ceto rayukansu. Guillaume Thibault/RFI
Talla

Jami’an tsaro sun ce bom na farko an boye shi ne cikin masallacin yayinda na biyu kuma a waje ajiye takalma.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin, amma sai dai ya jefa garin cikin rudani.

Ko a ranar 24 ga watan Junairu ma an kai makamancin wannan hari a kan masallatan tare da hallaka kusan mutane 50.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.