Isa ga babban shafi
Afrika

Tsarin fasalta siyasar Afrika ta bangaren tsaro da yaki da cin hanci

Yau litinin Shugabannin kasashen Afirka ke ci gaba da taron su a Addis Ababa, inda ake saran zasu mayar da hankali kan shirin yaki da cin hanci da rashawa.Tuni kungiyar ta bayyana nada shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a matsayin wanda zai jagoranci yakin, kuma shi ake saran ya jagoranci zaman taron na yau.

Antonio Guterres, Sakatary Majalisar Dinkin Duniya
Antonio Guterres, Sakatary Majalisar Dinkin Duniya RFI/Richard Riffonneau
Talla

A daya bangaren Sakatary Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana damuwar sa gani kalubale da  dakarun wanzar da zaman lahiya ke fuskanta a Nahiyar Afrika wajen gudanar da ayyukan su.

Guterres ya bukaci kasashen Afrika su bayar da hadin kai a kokarin su na yakar kungiyoyin dake dauke da makamai. Lamarin dake kawo koma baya ga kokarin majalisar Dinkin Duniya na  wanzar da zaman lahiya a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.