Isa ga babban shafi
Senegal

'Yan kasar Senegal sun lashe tallafin samun horon aikin Jarida

An sanar da sunayen wadanda suka lashe tukuicin samun horo a karkashin gasar da aka yi wa taken ‘’Ghislaine Dupont da kuma Claude Verlon’’, ma’aikatan Radio France International da ‘yan ta’adda suka kashe a Mali shekaru 4 da suka gabata.

Marie-Christine Saragosse shugabar kafafen yada labaran Faransa, da Cécile Mégie babbar Darakatar rfi, tare da 'yan kasar Senegal da aka karrama da basu kyautar tallafin bada horo a aikin jarida, yayin bikin da ya gudana ba daba tallafin a Senegal
Marie-Christine Saragosse shugabar kafafen yada labaran Faransa, da Cécile Mégie babbar Darakatar rfi, tare da 'yan kasar Senegal da aka karrama da basu kyautar tallafin bada horo a aikin jarida, yayin bikin da ya gudana ba daba tallafin a Senegal © Abdoulaye Diaw
Talla

An bayar da tukuicin ne ga wani dan jarida mai suna Arouna Diof da kuma wani Injiniyan daukar sauti mai suna Nicole Diedhiou, lokacin wani biki da aka gudanar a birnin Dakar na kasar Senegal.

Shugabar kafafen yada labaran Faransa da ke yada shirye-shirye zuwa kasashen ketare Marie-Christine Saragosse, ta ce matakin bada tukuicin shi ne nunawa ‘yan ta’adda cewa har abada ba zasu iya sanya yawa ‘yan jarida gwiwa ba.

Wannan ne karo na hudu da za a bayar da wannan dama ga dan jarida daya da kuma jami’in daukar sautin rediyo daga kasashen Afrika renon Faransa, a bikin da ya samu halartar Marie-Christine Saragosse shugabar kafafen yada labaran Faransa da ke watsa shirye-shirye zuwa ketare, da Cécile Mégie babbar Darakatar rfi, da kuma ‘yan uwa da dangin Ghislaine Dupont da Claude Verlon.

A Karon farko dai an sanar da sakamakon gasar ne a kasar Mali, sai na biyu a Madagascar yayin da a bara aka sanar da sakamakon a Jamhuriyar Benin.

Ana dai gudanar bikin ne a ranar da aka kebe domin kawo karshen cin zarafin ‘yan jarida a duniya.

A shekara ta 2014 ne aka kashe ma’aikatan na Radio France International a kusa da garin Kidal na arewacin Mali, a daidai lokacin da suke gudanar aikinsu.

A daidai lokacin da aka cika shekaru hudu da faruwar wannan lamari ne aka samu bayanan da ke tabbatar da cewa biyu daga cikin mutane ukun da ake zargi da aikata kisan na zaune ne a cikin kasar Algeria.

01:07

'Yan kasar Senegal sun lashe tallafin samun horon aikin Jarida

Nura Ado Suleiman

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.