Hukumar zaben Kenya ta sallami manyan jami'anta.
Hukumar zaben Kenya ta sauke wasu daga cikin manyan jami’anta 7 daga bakin aiki, tare da maye gurbinsu da wasu daban. Matakin dai na zuwa ne bayan sharuddan da jagoran adawa Raila Odinga ya gindaya kafin amincewa ya sake fitowa a zaben kasar na watan Oktoba da kotu ta sanya.
Wallafawa ranar:
Hukumar zaben ta sauya Daraktan fasahar sadarwa na ICT James Muhati da Albert Gogo, sai kuma Mr Marjan Hussein Marjan daraktan kula da shirye-shiryen hukumar yayinda Dr Sidney Namulungu zai jagoranci bangaren gudanarwa.
Sauran sun hada da Ms Nancy Kariui a matsayin shugabar sashen samar da kayayyakin zabe da kuma Mr Bernard Misati Moseti a matsayin shugabar sashen bayar da horo na hukumar.
A cewar shugaban hukumar Mr Chebukati, dukkanin nade naden za su fara aiki nan ta ke har zuwa watanni uku masu zuwa bayan kammala zaben kasar da kotu ta sanya ya gudana cikin watan Oktoba mai zuwa.
Matakin sauya manyan jami’an hukumar zaben dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan Jagoran adawa Raila Odinga ya gindaya sharuddan cewa ba zai shigo a dama da shi a zaben kasar ba, matukar ba a sauya wasu daga cikin jami’an hukumar ba.
Matakin da a baya wasu ke kallo a matsayin abin da ba zai yiwu ba, la'akari da cewa dukkanin jami'an hukumar gwamnati mai ci ta Uhuru Kenyatta ce ta nada su kan mukaman da su ke.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu