Isa ga babban shafi
Bakin-haure

''Masu fasa-kwauri sun jefa baki 50 a teku''

Kungiyar da ke sa ido kan kaurar baki ta Majalisar Dinkin Duniya, IOM, ta ce da gan-gan aka jefa wasu baki 50 ‘yan Afirka da suka nitse a cikin teku jiya laraba a mashigin ruwan kasar Yemen daga cikin baki 120 da ke cikin wani jirgin ruwa.

Bakin-haure na ci gaba da mutuwa a Teku
Bakin-haure na ci gaba da mutuwa a Teku Patrick Bar / SOS Méditerranée
Talla

Laurent de Boeck, jami’in kungiyar da ke Yemen ya ce wadanda suka tsira daga cikin bakin sun shaidawa abokan aikin su a gabar ruwan Yemen abinda ya faru.

Jami’in ya ce tuni masu safarar bakin suka koma Somalia domin ci gaba da yaudarar masu neman tsallaka nahiyar Turai suna hallaka su a teku.

Kungiyar ta ce ta gano gawawakin baki 29 daga cikin su a Shabwa da ke Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.