Isa ga babban shafi
Najeriya

Sakon Buhari na Sallah da Hausa ya janyo cece-kuce a Najeriya

Sakon barka da Sallah da shugaba Muhammadu Buhari ya aikawa ‘Yan Najeriya da harshen Hausa ya janyo cece-kuce da muhawara a kasar inda wasu ke ganin da harshen kasa na Ingilishi ya kamata shugaban ya yi amfani da shi.

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari AFP via telegraph
Talla

Sakon na tsawon minti daya da Sha’aban Ibrahim Sharada mai taimakawa Buhari wajen watsa labarai ya aikawa manema labarai a jajibirin Sallah shi ne na farko tun lokacin da shugaban ya koma London domin diba lafiyarsa.

Shugaban ya yi wa ‘yan Najeriya godiya dangane da irin addu’o’in da suke yi masa na fatan samun lafiya.

Sannan a sakon ya yi kira ga hadin kai da guje wa yada kiyayya a tsakanin ‘yan kasa.

Wasu rahotanni sun ce gwamnati ta fitar da sakon muryar ne domin yin watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa rashin lafiyar da ke damun shugaban har ta kai ba ya iya magana.

Sai dai harshen Hausa da shugaban ya yi amfani da shi a sakon ya janyo cece-kuce da muhawara a Najeriya, inda wasu ke ganin Ingilishi ne harshen kasa da shugaban ya kamata ya aikawa ‘yan Najeriya da sakon.

01:07

Jaafar Jaafar Mai sharhi kan lamurran yau da kullum

Galibin mutanen arewacin kasar na magana ne da harshen hausa, yayin da kudancin kasar ke magana da harshen Yoruba da Igbo.

Wasu daga kudancin kasar sun soki shugaban da nuna banbanci ta hanyar mutunta harshen hausa da wani bangare na Najeriya tare da caccakar masu taimaka masa a fannin watsa labarai da har suka amince ya yi magana da harshen hausa a matsayin sako ga ‘Yan Najeriya.

Sakon muryar Buhari da Hausa

 

 

Ga abinda wasu suka rubuta a twitter

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.