Isa ga babban shafi
Najeriya

DW ta damu kan ma’aikacinta da ‘Yan sanda suka ba kashi a Kaduna

Hukumar gudanarwa ta gidan rediyo da talabijin ta Deutsche Welle mallakin gwamantin Jamus, ta aike wa gwamnatin Najeriya da wasikar nuna damuwa, dangane da yadda ‘yan sanda suka kama tare da dukan daya daga cikin wakilan tashar Ibrahim Yakubu a garin kaduna.

Tambarin Deutsche Welle
Tambarin Deutsche Welle
Talla

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da ta gabata, lokacin da dan jaridar ke daukar rahoton yadda mabiya Shi’a ke gudanar da muzahara.

DW ta ce ‘Yan sandan na Najeriya sun tilasta wa wakilinta ya amsa cewa shi ma dan Shi’a ne, tare da farfasa kayan aikinsa.

An dai haramtawa Shi’a yin muzahara a Kaduna, tun rikicin mabiya Zakzaky da sojojin Najeriya.

Rahotanni sun ce ‘yan sandan sun yi harbi sama tare da harba tiyagas domin tarwatsa taron mabiya shi’ar a ranar Juma'a.

Wata majiya daga inda al’amarin ya faru ta shaidawa RFI Hausa cewa rikici tsakanin ‘yan sandan da wakilin na DW ya faru ne saboda ba ya da katin shaida da zai tabbatar da dan jarida ne ko kafar yada labaran da ya ke wa aiki.

A cikin wata wasika da ta aikewa gwamnatin Najeriya, Hukumar gudanarwar Deutsche Welle ta bukaci hukunta ‘yan sandan da suka ci zarafin Ibrahim.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.