Human Rights Watch ta zargi sojojin Uganda da ci zarafin mata
Kungiyar Agaji ta Human Rights Watch ta yi zargin cewar sojojin kasar Uganda dake aikin samar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma ke farautar shugaban Yan Tawaye Joseph Kony sun ci zarafin mata da 'Yan mata 13.
Wallafawa ranar:
Kungiyar ta ce ta samu hira da mata sama da dozen guda da suka yi wannan zargi cewar sojojin sai sun yi lalata da su kafin su basu abinda zasu ci, kuma sun tabbatar da aukuwar lamarin.
Wasu daga cikin Yan matan sun ce yanzu haka suna dauke da juna biyu sakamakon cin zarafin.
Richard Karemire, mai Magana da yawun sojin Uganda ya ce suna gudanar da bincike a kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu