Isa ga babban shafi
Ghana

Ghana za ta tura dakaru 205 zuwa Gambia

Shugaban Ghana Nana Akufu-Addo ya sanar da matakin tura dakaru 205 zuwa kasar Gambia daga cikin rundunar sojojin Afrika da za su yaki Yahya Jammeh. Tuni Najeriya ta sanar da tura dakaru 200 da jiragen yaki, yayin da sojojin Senegal suka kewaye kan iyakokin Gambia.

Zababben shugaban Gambia Adama Barrow
Zababben shugaban Gambia Adama Barrow STR / AFP
Talla

Da misalin karfe 4 na yau Alhamis ake sa ran rantsar da Adama Barrow a Senegal wanda ya doke Yahya Jammeh a zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Disemba.

Amma Jammeh wanda ya shafe shekaru 22 yana mulki a kasar ya ki amincewa da sakamakon zaben tare da kaddamar da dokar ta baci.

Sai dai kuma rahotanni sun ce babban hafsan sojin Gambia ya ce ba zai yi wasa da rayukan sojojin shi ba, wanda ke nuna ba za su yi fada da dakarun Afrika ba.

Daruruwan mutanen Gambia ne suka tsere zuwa Senegal saboda fargabar ballewar yakin basasa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.